<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>45</hymn_number>
<title>Ya Yesu, Muna Jiranka LW45</title>
<lyrics>[V1]
 1) Ya Yesu, muna jiranka,
 Da ikonka na warkarwa.
 Ba mu da ikon taimako.
 Ka cika dukanmu yanzu.

[V2]
 2) Ka ji mu, muna nemanka.
 Ba duk a nan sun san ka ba.
 Mun sani kana nemansu.
 Jawo su duk, Mai ƙaunarmu.

[V3]
 3) Kai ne mai sanin cutarmu,
 Mai gyara mugun tunani.
 Tone ƃoyayyun laifofi,
 Mai Fansarmu kan giciye.

[V4]
 4) Ka cire ƙarin mutuwa,
 Ka kau da aikin maciji.
 A cikinmu, yi nasara
 Don mulkinka madauwami.

[V5]
 5) Ka dubi masu ƙunci yau.
 Rinjayi duk ƴan kangara.
 Ka kwance ƙangin ɗaurarru,
 Ka mai da su a hanyarka.

[V6]
 6) Ya Almasihu, Ɗan Mutum,
 Ka ɗauki tabi'armu da,
 Alherinka mai yawa ne,
 Mai Cetonmu, Mai Gafara.

[V7]
 7) Kai ne da ikon warkarwa,
 Da yau da kullum kamar da.
 Ka ji mu yau, Maɗaukaki,
 Warkad da mu da hannunka.</lyrics>
</song>